IQNA

Hadarin ‘Yan Ta’adda Babbar Barazana ce Ga Karamar Manzon Allah (SAW)

23:37 - January 10, 2015
Lambar Labari: 2694072
Bangaren kasa da kasa, Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar hatsarin ‘yan takfiriyya masu kafirta musulmi ya isa zuwa kasashen da suka kirkiro su da turo su zuwa kasashen yankin Gabas ta tsakiya, yana mai kira al’ummar musulmi da su hada karfi da karfe wajen fada da wadannan mutanen.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin Al-manar cewa, Sayyid Nasrallah ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya gabatar a yammacin yau wajen bikin maulidin Annabi (s.a.w.a) da Jikansa Imam Sadiq (a.s) da makon hadin kai da aka gudanar a kasar ta Labanon inda ya ce ‘yan takfiriyyan suna ci gaba da bata sunan Musulunci da Manzon Allah da sauran Annabawa da Manzannin Allah ta hanyar ayyukan da suke aikatawa da suka hada da zubar da jinin mutanen da ba su ci ba su sha ba.
Shugaban na Hizbullah ya kara da cewa cutarwar da wadannan kungiyoyi suke yi wa Musulunci ba shi da tamka cikin tarihi. Don haka ya ce wajibi ne  al’ummar musulmi da dukkanin mazhabobinsu su hada hannu waje guda wajen fada da wadannan mutanen.
A wani bangare na jawabin nasa, Sayyid Hasan Nasrallah yayi kakkausar suka ga gwamnatin Bahrain saboda irin zaluncin da take yi wa al’ummar kasar da suka fito don neman hakkinsu.
A hakikanin gaskiya duk wanda ya kalli abin da ke faruwa a kasashen musulmi na daga abubuwan da mutanen da ake kokarin nuna su a matsayin masu kishin Musulunci suke aikatawa, lalle babu yadda zai yi face ya iya fahimtar dalilan da ya sanya wasu suke tambayar kansu cewa kai wannan wani irin addini ne wanda ba abin da ya sa a gaba in ban da ‘yanka mutane’ ‘keta kiraza da cin zuciya’ ‘tada bama-bamai a tsakanin al’umma da kashe mutanen da ba su ci ba su sha ba’ da sauransu.
A nan wajibi ne a sake jinjinawa wa marigayi Imam wanda ya zo da kuma gabatar wa da duniya da Musulunci na hakika na Annabi Muhammadu, Musuluncin da ke ganin dan’adam a matsayin “ko dai dan’uwanka ne a addini ko kuma tsaranka a halitta.
To a nan dai wajibi ne mu tambayi kanmu, wai ina ne matsalar take Daga ina wannan tunani da akidar “gaya wa jini na wuce’ wacce ba abin da ta sa a gaba in ban da bakanta sunan Musulunci, ta samo asali?
To amsa wannan tambayar dai ba abu ne mai wahala ba.
Dukkaninmu za mu iya tuna cewa yaduwar akidar wahabiyanci mai kafirta musulmi a duniya ta tsananta ne bayan mamayar da tsohuwar Tarayyar Sobiyeti ta yi wa kasar Afghanistan, haka nan da kuma nasarar da juyin juya halin Musulunci ya samu a kasar Iran a shekarar alhali kafin wannan lokacin wannan akida ta takaita ne kawai tsakanin Saudiyya da Pakistan da wani bangare na kasar Masar wato an kara karfafa akidar ce don dushe hasken juyin da kuma fada da Tarayyar Sobiyetin.
An fara yada wannan akidar ce a lokacin da Amurka ta bukaci Saudiyya da ta taimakawa kungiyoyin kasar Afghanistan wajen fada da Tarayyar Sobiyeti, kamar yadda kuma ta bukaci karin taimakon kasashen Pakistan da Masar da Jordan, manyan kawayen kasashen yammaci a yankin don cimma wannan manufa saboda a lokacin kasar Turkiyya tana fama da rikice-rikicen cikin gida, ita kuwa kasar Iraki tana fama da yakin da ta kallafa wa Iran.
A wancan lokacin ne aka kafa tushen kungiyar Taliban da Al-Ka’ida da sauran kungiyoyi masu kafirta musulmi a dukkanin kasashen musulmi. To sai dai Amurka da Saudiyya da Pakistan wani abu na daban suke tunani wanda shi ne samar da wata jama’a wacce a nan gaba za a iya amfani da ita cikin duk wani rikici da gasa da zai hada su da wasu kasashen duniya ko kuma na yankin Gabas ta tsakiya.
Dukkanin bayanai da dalilai da babu kokwanto cikinsu suna nuni da cewa kungiyoyi irin su Taliban da Al-Ka’ida da makamantansu sun ginu ne bisa wasu tushe guda biyu:
Bukatar da Amurka da kasashen yammaci suke da ita na samun wata kafa ta cutarwa da kuma yin barazana ga tsaron kasashen Rasha da China da kuma kirkiro wani salon Musulunci dan jagu don fada da Musulunci na hakika wanda marigayi Imam ya tabbatar da shi a kasar Iran wanda ya ginu bisa akida da koyarwar fikihun mazhabar Ja’afariyya Ithna Ashariyya. Ko shakka babu nasarar wannan juyi a Iran ya shammaci kasashen yammaci da kuma sauya dukkanin tunani da tsare-tsaren da suka yi a yankin Gabas ta tsakiya.
Akida da fatawoyin’tsoffin Najadu’ da makudan kudaden kasashen yankin Tekun Fasha da kuma kwarewa ta yaki da leken asiri irin na kasashen Masar da Pakistan da Jordan da sauransu.
Daga bayanan da suka gabata, ana iya cewa maganar fada da ta’addanci da tsaurin ra’ayi da Amurka take cewa tana yi wani ‘zuki ta malle’ ne, don kuwa maslahar Amurka da kasashen yammaci tana tare da samuwar irin wadannan kungiyoyi masu alaka da kungiyar leken asirin Amurka da sauran kungiyoyin leken asiri na kasa da kasa.

2688566

Abubuwan Da Ya Shafa: Nasrullah
captcha