IQNA

Kalma Biyu Daga Sayyid Nastullah Zuwa Ga Yahudawa ‘Yan Mamaya

16:46 - January 20, 2015
Lambar Labari: 2736736
Bangaren kasa da kasa, jagoran kungiyar Hizbullah a Lebanon ya aike da sako ga yahudawan sahyuniya yan mamaya da cewa su tanadi wasu wurare buya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Almanar cewa, an nuna hoton shugaban kungiyar Hizbullah a Lebanon Sayyid Hassan Nasrulah yana aike wa da sako ga yahudawan sahyuniya ta hanyar ishara da yatsu da da magana ba da cewa yan mamaya su tanadi wasu wurare buya a lokuta masu zuwa.
Kungiyar ta Hizbullah ta kasar Labanon ta sanar da cewa ko shakka babu za ta mayar da martani ga harin da jiragen yakin Haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai yankin Qunetra na kasar Siriya da yayi sanadiyyar shahadar shida  daga cikin dakarun ta, tana mai cewa martanin kuwa za ta zamanto mai tsanani da cutarwa ga Haramtacciyar kasar Isra’ila saboda wannan wauta da ta yi.
A wata hira da yayi da tashar talabijin din Al-Alam da ke watsa shirye-shiryenta daga birnin Tehran, na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, na’ibin shugaban majalisar siyasa ta kungiyar Hizbullah din ya ce martanin da kungiyar za ta kai ga wannan wauta na Haramtacciyar kasar Isra’ila zai zamanto mai tsananin gaske.
Jami’in kungiyar ta Hizbullah ya kara da kungiyar ce za ta zabi lokaci da kuma wajen da ya dace ta mayar da wannan martanin, yana mai cewa ko shakka babu zai zamanto mai tsanani da kuma cutarwa ga Haramtacciyar kasar Isra’ila n.
Tun dai bayan harin da jiragen yakin Haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai yankin Qunetra na kasar Siriyan gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra’ila take cikin tsananin damuwa saboda tunanin martanin da Hizbullah din za ta mayar wanda kafafen watsa labaran Haramtacciyar kasar Isra’ila suka ce ko shakka babu za ta mayar.
2734307

Abubuwan Da Ya Shafa: Nasrullah
captcha