IQNA

Ministan Harkokin Wajen Jamus Ya Sanar Da Hana Yada Zanen Batunci Ga Manzon Allah

23:13 - January 25, 2015
Lambar Labari: 2764390
Bangaren kasa da kasa, ministan harkokin wajen kasar Jamus Frank Valter ya sanar da wata doka da ke hana yada zanen batunci ga manzon addinin muslunci a kasar.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ina cewa Shetain Mayer ministan harkokin wajen Jamus a lokacin da yake jawabi a gaban mambobin cibiyar Almanar ya sanar da wata doka da ke hana yada zanen batunci ga manzon addinin muslunci a kasar baki daya, tare da bayyana hakan cin zarafi ne ga wani bangare na al’umma.
Ita ma anata bangaren shugabar gwamnatin kasar Jamus ta bayyana cewa addinin muslunci da musulmi wani bangare ne al’ummar kasar Jamus ya zama wajibi a tafi tare da su tare da nuna rashin amincewa da duk wani matakin tsangwama a kansu domin su bangare na al’ummar kasa.
Fiye da mutane dubu talatin da biyar sun gudanar da zanga-zanga a jiya a kasar Jamus domin nuna rashin amincewarsu da tsangwamar da ake nuna ma musulmi a cikin kasashen turai musamman ma a kasar ta Jamus.
Mataki da mahukuntan kasar ta Jamus suka dauka na nuna rashin amincewa da duk wani mataki na takura mabiya addinin muslunci ya harzuka masu tsatsauran ra’ayin kiyayya da musulmi, da ke neman a kori duk wani musulmi daga kasar, bisa hujjar cewa akasarin musulmin kasar baki ne.
Haka nan kuma addinin muslunci bakon addini ne a kasar da ba za su amince da shi ba.
A cikin shekara ta dubu biyu da goma shugabar gwamnatin Jamus ta fadi irin wannan magana, tare da bayyana cewa a kowane lokaci mabiya addinin muslunbci suna iko da ‘yancin da su gudanar da harkokin addininsu a kasar.
2762264

Abubuwan Da Ya Shafa: jamus
captcha