Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ATLASINFO.FR cewa, bangarorin da suka taru sun ajiye a kan cewa za a gudanar da wasu tarukan makamantan wannan a majami’oin Ranto da kuma Santo Antonio dake cikin birnin Lisbon, tare da halartar dukkanin bangarorin addinan da suka taru a masallacin.
Khoze Aulman babban jagoran mabiya addinin yahudanci a kasar ta Portugal ya bayyana cewa wadannan addinai guda uku suna da abubuwan da suka hada su, wadanda sun fi abubuwan da suka raba su yawa, a kan haka dole ne su raya su domin samun fahimtar juna da zaman lafiya tare a tsakanin dukkanin mabiya wadannan addinai.
Shi ma a nasa bangaren jagoran mabiya addinin kirista na darikar Katholika ya bayyana cewa wanna taro yan ada matukar muhimmanci, kuma majami’arsa za ta dauki nauyin shirya taro nag aba domin haduwa a tsakanin mabiya addinai na sama domin yin addu’a ta zaman lafiya da sulhu a tsakaninsu.
A nasu bangaren mabiya addinin Hundus sun gudanar da nasu tarukan da addu’oin a wani babban daki da suke yin harkokin ibadarsu, inda a can ma suka yi addu’a bayan kai harin birnin Paris.
2763346