IQNA

Ministan Kula Da Harkokin Addini A Syria Ya Ce Malami Suna Da Bbaban Aiki A Gabansu

20:38 - March 13, 2015
Lambar Labari: 2975581
Bangaren kasa da kasa, minister mai kula da harkokin addini a kasar Syria Abdulsattar Sayyid ya bayyana cewa malaman addinin muslunci suna da gagarumin aiki a gabansu na wayar da kan mutane.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Tashrin cewa, Muhammad Abdulsattar Sayyid ministar mai kula da harkokin addini a kasar Syria ya bayyana cewa malaman addinin muslunci suna da gagarumin aiki a gabansu na wayar da kan mutane dangane da hakinin muslunci da koyarwarsa.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a gaban wani babban taro na manyan malamai da limamai na birnin Damscus fadar mulkin kasar ta Syria, wanda ake gudanarwa  akowace shekara domin yin bita kan ayyukan da suka jibinci malaman addini.
Dangane da irin hadarin da al’umma ke fuskanta na ta’addanci, ya bayyana cewa a koda yaushe malamai suke da hakkin shiryar da mutane a duk lokacin da suka shiga fangima da rashin sanin inda za su dosa, haka nan kuma malamai su ne su ne kan gaba a kowane lokaci wajen bayar da haske a cikin addini tare da haska ma mutane daga abin da suka sani na ilimin addini.
Malaman da suka gabatar da jawabi sun jaddada wajabcin yin aiki tare da juna domin fuskantar kalu balen da ke gaban al’ummar musulmi a wannan lokaci, tare da shan alwashin tunkarar duk wani mai son batar da al’umma da fatawoyi na shirme da jahilci da gangan ko bisa sani.
2973515

Abubuwan Da Ya Shafa: syria
captcha