Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Al-manar cewa, a jawabin da ya gabatar wanda tashoshin talabijin na cikin gida da waje suka watsa kai tsaye, Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa ina jiragen yakin masarautar Saudiyyah da sauran kasashen larabawa da ta dauka haya suke duk tsawon shekarun nan da Isra'ila ta kwashe tana kashe musulmi 'yan sunnah a Palestinu?
Ta yaya gwamnatocin Iran da Syria ne kawai ke taimaka ma palastinawa me ya kawo Amurka da Isra'ila wajen kare 'yan sunnah a Yemen? Mata da kanan yara da tsoffi da masarautar Saudiyya ke kashewa a halin yanzu a Yemen wadanda su ba 'yan shi'a ba ne kuma su ba 'yan Al-Huthi ba ne, su kuma mene ne laifinsu.
Mene ne yasa masarautar Saudiyyah ba za ta mayar da hankali wajen hada kan al'ummar musulmi da fifita maslahar musulunci da al'ummar musumi baki daya a koda yaushe ba, wanda kuma wannan shi ne sunnar manzon Allah maimakon hankoron haifar da fitina tsakanin al'ummar musulmi da hada su yaki da kafirta juna saboda banbancin fahimta? Idan al'ummar musulmi ta tarwatse shin wane ne zai yi farin ciki da hakan? Manzon Allah ko kuwa Amurka da Isra'ila da sauran makiya musulunci.
Ya ci gaba da cewa a kowane lkaci masarautar Saudiyya da sauran masu yi mata amshin shata gami da wasu gwamnatocin yankin suna yin amfanin da dukkanin abin da suke da shi wajen kare manufar iyayen gidansu ne kawai, abin ban takaicin kuma shi ne yadda suka danganta barnar da suka yi da addini, wanda kuma hakan a cewarsa abu ne mai matukar muni.
Sayyid Nasrullah ya kara da cewa kasashe irin su Turkiya da Qatar tare da hadin gwiwa da masaurar saudiyya da kuma sauran kasashe makiya sun yi amfani da dkkanin karfinsu wajen tunkarar gwamnatin Syria domin kifar da ita, amma hakan ta ci tura, a kan hakan suna neman wata hanyar da za su fanshe kayin da suka sha.
3050311