IQNA

Al Saud Za Su Sha Kayi A Yemen/Daesh Da Wahabiyanci Su Ne Barazana Haramai Biyu

23:56 - April 18, 2015
Lambar Labari: 3169192
Bangaren kasa da kasa, babban sakataen kungiyar Hibullah a kasar Lebanon ya yi shara da irin hadarin da ke tatatre da hankoron da wahabiyawa na rarraba kan al'ummar musulmi ta hanyar yada rikicin shi'a da sunna a tsakanin musulmi wanda kuma hakan bai yi nasara ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Almanar cewa, Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, Sayyid Hasan Nasrallah ya sake jaddada matsayar kungiyar Hizbullah din ta nuna rashin amincewa da kuma Allah wadai da hare-haren wuce gona da iri da Saudiyya bisa goyon bayan Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila suke yi kan al’ummar kasar Yemen, yana mai sake jaddada goyon bayansu ga al’ummar ta Yemen.
Sayyid Nasrallah ya bayyana hakan ne a jawabin da yayi wajen taron da kungiyar ta shirya don nuna goyon baya ga al’ummar kasar Yemen da aka gudanar a birnin Beirut, babban birnin kasar Labanon inda ya ce: Mun dau wannan matsayar ce saboda muna ganin hakan a matsayin wani wajibi na addini da shari’a da kuma kyawawan halaye na dan’adamtaka. Don haka ne Sayyid Nasrallah ya kirayi dukkanin al’umma da su goyi bayan hakan yana mai cewa: Mu dai babu wani abin da zai hana mu daukar wannan matsayar ta ci gaba da yin Allah wadai da wannan wuce gona da iri na Saudiyya da Amurka a kan al’ummar kasar Yemen da kuma goyon bayan al’ummar kasar Yemen da ake zalunta, wacce da yardar Allah za ta yi nasara.
Sayyid Nasrallah ya kara da cewa: Lalle muna da nauyi a gaban Allah kuma za a yi mana hisabi kan matsaya da nauyin da muka dauka a wannan lokaci mai muhimmanci da cike da tarihi a kan dukkanin al’ummar wannan yankin.
Yayin da yake magana kan manufofin wannan yaki kamar yadda mahukuntan Saudiyyan da masu goya musu baya suka sanar, Sayyid Nasrallah cewa yayi: Masu wuce gona da iri a kan Yemen suna cewa wannan yaki ne na larabawa sannan kuma don kare larabci a kasar Yemen. Daga nan sai yayi tambayar cewa: Shin al’ummar larabawa ne suka ba wa gwamnatin Saudiyya izinin kai hari kasar Yemen? Idan har al’ummar Yemen ba su zama larabawa ba, to su waye larabawan?. Daga nan sai ya ce: Masu wuce gona da iri kan al’ummar Yemen ne ya wajaba su nemo shaida kan Musulunci da kuma kasantuwarsu larabawa. Sayyid Nasrallah ya ci gaba da cewa: Sun yi kokarin jingina yakin da cewa yaki ne tsakanin Sunna da Shi’a, alhali kuwa wannan yakin, wani wuce gona da iri ne da Saudiyya take yi a kan kasar Yemen don cimma manufofi na siyasa.
A ci gaba da karin haske kan dalilan yakin da aka sanar da kuma rashin gaskiya cikin hakan, Sayyid Nasrallah ya ce: Masu wuce gona da irin suna kokari nuna cewa haramomin Makka da Madina (Dakin Ka’aba da masallacin Annabi) suna cikin hatsari. Daga nan sai ya yi tambayar cewa: Waye yake barazana ga wadannan haramomin guda biyu? Shin mutanen Yemen ne, ko kuma sojojin Yemen?. Sayyid Nasrallah ya ce mutanen Yemen dai masu tsananin son Manzon Allah (s.a.w.a) da Ahlulbaitinsa ne. Don haka sai ya ce: Masallaci da kabarin Annabi suna fuskantar barazana daga cikin kasar Saudiyya ne, sannan kuma daga tunani da kuma akidar wahabiyanci ne, wanda littafan tarihi za su shaidi hakan. Sayyid ya ci gaba da cewa: “Akwai babbar barazana da wadannan haramomi guda biyu masu tsarki suke fuskanta daga wajen kungiyar ta’addancin nan ta Da’esh (ISIS) saboda kuwa suna ganin Dakin Ka’aba a matsayin wasu tarin duwatsu ne da ake bauta musu sabanin Ubangiji wanda hakan ya saba wa tauhidinsu”.
Yayin da yake mayar da martani ga dalili na gaba na kaddamar da wannan hari da Saudiyyan take fadi na cewa tana kai harin ne don kare al’ummar Yemen, Sayyid Nasrallah yayi tambayar cewa: “Shin kare al’ummar Yemen din shi ne zubar da a zubar da jininsu?. Sayyid Nasrallah ya ci gaba da cewa: “Mai yiyuwa ne mutanen Labanon za su iya tuna yakin 2006 da kuma kwatanta tsakanin wadannan yakukuwa biyu, wato yakin Saudiyya a kan Yemen da yakin Isra’ila a kan Labanon:, Sayyid Nasrallah ya ci gaba da cewa: “Mun kasance masu taran aradu da ka (kamar yadda Saudiyyan ta siffanta Hizbullah a lokacin yakin 2006 din) amma kuma mun yi nasara”.
Sayyid Nasrallah ya ce: “Saudiyya ta gaza wajen cimma kowane guda daga cikin manufofinta, don haka ne ta fara saukowakasa kasa dangane da manufofin da tace tana son cimmawa”. Sayyid ya ci gaba da cewa: “Abin ban dariya ne yadda mataimakin Abd Rabbuh Mansur Hadi, wato Khalid al-Bahah ya ke kiran sojojin Saudiyya da kada su shigo cikin kasar Yemen din”.
Har ila yau yayin da yake magana kan ci gaba da rashin nasarar da Saudiyya take fuskanta a yayin wannan wuce gona da irin nata, Sayyid Nasrallah ya ce: “Sakamakon harin wuce gona da iri kan Yemen shi ne tsayin dakan da Yemen ta yi, al’umma da sojojin kasar, bugu da kari kan hakurinsu; suna ci gaba da zanga-zanga duk kuwa da ruwan bama-bamai da kuma shirin ci gaba da yaki na tsawon lokaci”.
Sayyid Nasrallah ya ci gaba da cewa: “Wannan hari ya gaza wajen mayar da wannan yaki, yaki na cikin gida tsakanin mabiya mazhabar Zaidiyya da Shafi’iyya ko kuma tsakanin Shi’a da Sunna ko kuma tsakanin mutanen Kudanci da arewaci”. Sayyid Nasrallah ya ci gaba da cewa: “Kasar Saudiyya ta sha kashi cikin wannan wuce gona da iri nata, musamman hare-haren da take kai wa ta sama. Don haka ba su da wata mafita face su shigo kasar ta kasa, to a nan ne za mu ga abin da sojojin Saudiyyan za su iya yi”. Sayyid Nasrallah ya ci gaba da cewa: “Daga cikin dalilan da suke kawowa wajen halalta wannan wuce gona da irin shi ne cewa akwai yiyuwar barazana a kan Saudiyyan, to amma bayan wannan harin sai ga shi wannan barazanar ta tashi daga yanayi na mai yiyuwa, zuwa ga yanayi na babu kokwanto cikinsa”.
Sayyid Nasrallah ya ce: “Har ya zuwa yanzu mutanen Yemen ba su koma ga zabin da suke da shi ba ta yadda har ya zuwa yanzu ba su mayar da martani ba. Hakan hakuri ne na dabarar yaki”. Sayyid Nasrallah ya ci gaba da cewa: “Daga dukkan alamu gwamnatin Saudiyya ba shirya wa yarda da cimma yarjejeniya ba, duk kuwa da cewa akwai gwamnatoci masu yawa da suka nuna shirinsu, da sassautowa don neman mafita”. Sayyid Nasrallah ya ci gaba da cewa: Mafiya yawan gwamnatocin kasashen duniya suna adawa da wannan harin, don kuwa babu wani abin da mai zaluncin ya samu”. Sayyid ya kara da cewa: “Kwamitin tsaron da ake fatan zai samo mafita ga wannan yakin kan kasar Yemen, amma sai ga shi ya fitar da abin da ya fitar kwanaki biyun da suka gabata. Hakan kuwa da man shi ne abin da ake zaton gani. Hakan bai ba mu mamaki ba, kamar su ma mutanen Yemen din. Kudurin kwamitin tsaron ba shi da wata kima”.
Yayin da yake magana kan sakamakon yakin kuwa, Sayyid Nasrallah cewa yayi: “Ko shakka babu sakamakon yakin kasar Yemen shi ne shan kashin masu wuce gona da irin, dukkaninsu”.
Sayyid Nasrallah ya mika godiyarsa ga majalisar kasar Pakistan wanda ya hana sojojin kasar tafiya Yemen don yakar al’ummar Yemen kamar yadda Saudiyyan ta bukata. Daga nan sai ya kirayi al’ummomin “Pakistan da Masar” wanda ya ce sun taka gagarumar rawa wajen hana wahabiyawa rushe kabarin Annabi a shekarun baya da su taimaka wajen hana rusa wata kasar Larabawa da ta Musulunci. Har ila yau Sayyid Nasrallah ya bukaci kasashen larabawa da na musulmi da su tsoma baki wajen dakatar da dukkanin wadanda suke son ci gaba da wannan yakin a kan al’ummar Yemen da kuma tsamo kasar Yemen daga wannan bala'i da aka kirkiro shi da gangan.
Sayyid Nasrallah ya ci gaba da cewa: “Wasu mutane a kasar Labanon suna gani da kuma bayyanar sukar da ake yi wa Saudiyya a matsayin cin mutumcinta”. Don haka ya ce: “Duk da bayanan da muke da su kan irin rawar da Saudiyya a kasar Labanon a baya a lokacin yakin basasa da kuma rawar da take takawa a halin yanzu a Siriya da kuma shigowa kai tsaye wajen kashe mutanen Bahrain, amma duk da haka a kullum mun kasance muna kira zuwa ga tattaunawa. To amma a yau Saudiyya ta tashi daga tsoma baki ta hanyar amfani da wasu, a yau ita ce ta kaddamar da yakin”. Sayyid Nasrallah ya ce a yau Saudiyya ita ce take dagawa bayan kashin da ta sha a Labanon da Siriya da Iraki. Don haka a halin yanzu dai lokaci yayi da dukkanin kasashen larabawa da na musulmi za su tsaya su ce wa Saudiyya, lalle hakan ya isa.
Sayyid Nasrallah yayi tambayar cewa: “Waye yake gina makarantu a duk fadin duniya don su karantar da matasan musulmi tafarkin kafirta mutane da kuma ta’addanci. Saudiyya ce mai aikata hakan”. Sayyid ya ci gaba da cewa: “A saboda haka, ya zama wajibi kasashen larabawa da na musulmi su tsaya a gaban Saudiiya, su ce mata, lalle hakan ya isa”. Sayyid Nasrallah ya ci gaba da cewa: A yau muna fadin cewa, kasar Siriya muna godiya, saboda kin tsaya kyam, kin ki mika wuya ga ‘yan ta’adda masu kafirta mutane. Idan da ba don tsayin dakan Siriya da sojoji da al’ummar kasar ba, to da wani halin Labanon take ciki a halin yanzu?
Sayyid Nasrallah ya ci gaba da cewa: Lalle mu muna daga muryarmu sama wajen Allah wadai da wuce gona da irin (Saudiyya) a kan kasar Yemen da kuma yada ta’addanci. Babu wani abu a wannan duniyar, ko zagi ko barazana, da zai hana mu fadin hakan. Ku kira hakan da kowane sunan da kuke so, babu damuwa da yake murya ce saboda Allah”.
Sayyid Nasrallah ya ci gaba da cewa: “Za mu ci gaba da daga sautinmu duk kuwa da barazanar da ake yi”. Sayyid ya kara da cewa: “Babbar wacce za ta cutu da dukkanin abin da ke faruwa ita ce Palastinu, babbar mai cin ribar hakan kuwa ita ce Isra’ila”.
Sayyid ya ci gaba da cewa: “Yaudarar mutane da sunan haramai guda biyu, ya isa”. Sayyid Nasrallah ya ci gaba da cewa: “Mutanen Yemen za su ci gaba da tsayin daka, sannan kuma suna da kwarewa da kuma jagoranci da sojojin tsayayyu. Wanda yake da irin wannan siffar kuwa, ko shakka babu zai zamanto shi ne mai nasara”.
Daga karshe dai Sayyid Nasrallah ya kirayi sauran ‘yan sisayar kasar Labanon da su yi taka tsantsan kada su shigo da wannan rikici na Labanon cikin gidan Labanon din.
3161658

Abubuwan Da Ya Shafa: Nasrullah
captcha