Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na On Islam cewa, majalisar shawara ta musulmin nahiyar turai dake da mazauni a birnin Dublin na yankin Ireland ta sanar da cewa a ranar Talata za a haifi jinjirin wata.
Bayanin ya ce bisa la’akari da yanayi na sararinsamaniya a ranar Laraba ba za a ga watan ba, saboda, ranar Alhamis za ta zama daya watan Ramadan mai alfarma a nahiyar turai baki daya, kamar yadda kuma aka sanar da wanann bayani ga sauran musulmi na kasashe daban-daban da ke nahiyar.
A nasu bangaren mabiya addinin mulunci da ke zaune a cikin yankuna arewacin Amurka, wanda bayanin y yi daidai da wannan bayani da abin da majalisar ta musulmin nahiyar turai ta sanar a yau.
Bisa kididdigar da ibiyar Piva ta bayar, adadinin musulmin da suke zaune a cikin nahiyar urai a halin ya kai miliyan 44, wanda hakan shi ne kashi 6% na dukkanin adadinin mutanen nahiyar.
3311251