IQNA

Baje Kolin Kayayyakin Ramadan A Birnin Capetown Afirka Ta kudu

22:37 - June 09, 2015
Lambar Labari: 3312689
Bangaren kasa da kasa, A cikin wanann mako ne ake gudanar da wani baje kolin kayayyakin Ramadan a birnin Capetown na kasar Afirka ta kudu tare da halatar jama’a.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Anatoli cewa, yanzu haka ana gudanar da wani baje kolin kayayyakin Ramadan a birnin Capetown na kasar Afirka ta kudu tare da halatar jama’a daga bangarorin musulmi da ma wadanda ba su ba.

Daga cikin mutanen kasashen da suke halartar baje koin akwai yan kasashen India, palastinu, Jordan, Somalia, Masar, Turkiya, Spain da kuma Ireland.

Babbar manufar gudanar da wannan baje koli dai it ace kara bayyana wa sauran jama’a matsayin muslunci dangane da batutuwa da suka shafi msuulunci da kuma mahangarsa kan batutuwa da suka shafi zamantakewa jama’a.

Daga cikin abin ake mayar da hankali a kansa kamar kowace shekara akwai wayar da kan mutane musamamn ma wadanda ba musulmi ba, dangane da yadda ake nuna a ddinin muslunci, ta yadda ake yi masa mummunar fahimta.

Kasar Afirka ta kudu dai tana da mabiya addinin muslunci da suka kai kasha 2 cikin dari na dukkanin mutane miliyan 52 da suke zaune a fadin kasar.

3312405

Abubuwan Da Ya Shafa: Capetown
captcha