IQNA

Larabawa Na Bukatar Hadin Kasai Da Kuduri Na Siyasa Domin Fuskantar Matsalolinsu

23:44 - July 10, 2015
Lambar Labari: 3326313
Bangaren kasa da kasa, babban sakataren kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon ya bayyana cewa al’ummar larabawa na bukatar hadin kai da kuma kudiri na siyasa domin warware matsalilin da suke fama da su a yanzu.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-nashrah cewa, Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana a daren jiya a taron daren lailatull qadr cewa, wannan lokaci ne ake bukatar hadin kai a tsakakin al’ummomin larabawa domin fuskantar halin da suka samu kansu a ciki.

Wannan bayani nasa ya mayar da hankali kan muhimman lamurra da suka zama wajibi a mayar da hankali a kansu a wannan lokaci, inda ya ce akwai bukatar addua da kuma burin a siyasa tsakanin dukkanin bangarori na wannan al’umma.

Dangane da yakin da suka yin a tsawon kwanaki 33 kuwa  acikin shekara ta 2006, ya bayyana cewa wannan ya tababtar da nasar da suka samu daga ubangiji ne, kuma mutanen kasar Lebanon sheda ne kan hakan.

Babban sakataren na Hizbullah ya ce babban bala’in da ke damun al’umma a halin yanzu shi ne masu girman kai da kuma Isra’ila, sai kuma yan ta’addan takfiriyyah da suka kirkiro, wadanda suka zama wata bababr sankara ga musulmi da kiristoci.

3326132

Abubuwan Da Ya Shafa: lebanon
captcha