Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Arabi 21 cewa, Wasim Yusuf shi ne limamin masallacin Sheikh Zayid a birnin Abu Dhabi ya fadi cewa wasu daga wahabiyawa musamman Uraifi da Salman Audah suna da hannu wajen yada tunanin kungiyar ta’addanci a tsakanin larabawa.
Ya ce wani daga cikin masu tabligin wahabiyanci mai suna Hammud Al-umari ya kasance daya daga cikin masu wannan tunani tare da yada shi, kma an tsare shi a gidan Kason Abu Ghoraib da Al-taji a kasar Irakia shekara ta 2013, bayan ya fito kuma ya ci gaba da goyon bayan Abubakar Albaghdadi.
Wasim Yusuf ya kara da cewa, Al-uraifi yana goyon bayan akidar Daesh ta ta’addanci, haka nan kuma Salman Audah shi ma yana nuna goyon bayansa da hakan a fili.
3339662