IQNA

Laifukan Sahyuniya A Yankin Diffa Kisan Kiyashi Ne / Wajabcin Motsin Musulmi Da Larabawa

22:07 - August 09, 2015
Lambar Labari: 3340687
Bangaren kasa da kasa, Sayyid Ali Fadlollah Malami A Lebanon ya ce ayyukan zaluncin da yahudawan sahyuniya suka iawatarwa acikin yanknan palastinawa da ke gabar yamma da kogin jodan laifukan yaki da ya kamata a hukunta su a kansu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Almanar cewa, Sayyid Ali Fadlollah limamin Juma’a Beirut a jiya yabayya acewa, ya zama wajibi kan kasashen musulmi da na larabawa da su mike domin fskantar ayyuakan zaluncin yahudawan sahyuniya kan al’ummar palastinu.
Ya kara da cewa ayyukan zaluncin da yahudawan sahyuniya suka aiwatarwa a cikin yankunan palastinawa da ke gabar yamma da kogin jodan da kuma gabacin aqsa duk laifukan yaki da ya kamata a hukunta  su a kansu a kotun manyan laifuka ta duniya.
Sayyid Ali Fadlollah ya ce irin abin da yahudawan suke yin a cin zarafin fararen hula a cikin yankunan palastinawa na kisanb yara da mat aba gaira babu sabar, hakan ya sabawa dukkanin dokoki na duniya balantana koyarwar wani addini, a kan dole ne a grfanar da su domin su fuskanci sharia.
Dangane da yadda suke mamaye yankunan palastinawa kwa cewa ya yi, dukkanin abin da suke yi a kan idanun duniya suke yi, kuma al’ummomin da suke kwacewa yankunan sunan ana kallonsu suna watangaririya ba tare da dafa mus, wanda hakan ke nuni da cewa abin da suke suna da goyon bayan kasashen duniya.
Sayyid Ali Fadlollah y ace idan sauran kasashen yammacin trai masu mara baya ga yahudawa sun yi shiru kan wannan tabargaza, mene ne dalilin da zai sanya musulmi da larabawa su yi shiru kan hakan, wanda hakan ke nuni da cewa su ma wani bangare ne zaluncin.

 

3340291

Abubuwan Da Ya Shafa: lebanon
captcha