Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Anatoli cewa, Itayi vierry kakakin majalisar dinkin duniya ya yi tsokaci kan batun ayyukan yan gudun hijira inda ya bayyana cewa nuna banbancin addini da ake yi wa wasu masu neman gudun hijira ya saba wa dukkanin dokoki na duniya baki musaamn ma a bin da ake yi wa masu neman mafakar siyasa a nahiyar turai.
Ya kara da cewa ana nuna musu banbancin addini matuka saboda wata kila akasarinsu mabiya addinin muslunci ne yayin da kuma anahiyar akasarin mutane suna bin addinin kiristanci ne, alhali wannan bay a daga cikin abin doka ta kasa da kasa ta shata, dukkanin mutane ana yi musu kallon ‘yan adam ne ba tare da la’akari da addininsu ko akidarsu ba.
Ya ci wani abu mai ban takaici ya farua cikin ‘yan kwanakin na a Maqdonia, inda kasashen Cheque da kuma Solvakia suka ce za su karbi ‘yan gudun hijira na wadannan kasashe ne kawai idan mabiya addinin kirista ne, wanda kuma addininsa bah aka yake ba to sai dai ya nufi wurin na daban.