Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na hqmi.org cewa, wannan gasar hardar kur’ani mai tsarki an gudanar da ita ne tare da hadin gwiwa tsakanin cibiyar da kuma babbar cibiyar kula da lamurran hardar kur’ani ta duniya, tare da halartar mahardata 43 da suka shiga gasar.
An dai gudanar da gasar ne a babban masallacin Al-fatah da ke birnin Capetown na kasar Afirka ta kudu tare da halaratr Sheikh Riyad Fitar mataimakin shugaban kwamitin lamurran shari’ar muslunci a kasar, tare da wasu daga cikin wakilan kungiyoyin musulmi na kasar da suka samu halarta.
Bayanin ya ci gaba da cewa gasar ta gudana ne a dukkanin bangarori guda uku da aka sanar, wato hardar kur’ani baki daya, sai kuma rabinsa da kuma kashi daya bisa uku, inda aka bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka nuna kwazo.
Haka nan kuma an gudanar da bayanai na tunatarwa dangane da muhimmancin mayar da hankali ga lamurra da suka shafi kur’ani mai tsarki, da kuma yadda za a fa’idatu da shia cikin rayuwa.
3354490