Kamfanin dilalncin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Shafaqna cewa, a yau ne gwamnatin kasar Borkina Faso ta bada sanarwan makoki na kwanaki uku a fadin kasar wanda zai fara daga ranar gobe Juma’a.
Bayanin ya ci gaba da cewa sanadiyyar rasuwar mahajjatan kasar 22 da aka tabbatar da mutuwarsu a turmutsutsin ranar sallar layyar da ta gabata.
Kamfanin dillancin labaran faransa ya ce gwamnatin kasar ta bada wannan sanarwar ce bayan taron majalisar ministocin kasar a jiya laraba. Ta kuma kara da cewa ya zuwa ranar sha uku ga oktoba da muke ciki, mahajjatan kasar 22 aka tabbatar da mutuwarsu.
Sannan har yanzun akwai wasu guda 9 da suka bace banda haka sanarwar ta kara da cewa akwai wasu mahajjan 15 da suka rasu don rashin lafiya a lokacin aikin hajji na shekara da muke ciki.