Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Yaum Sabi cewa, Fedrica Mogerini babbar jami’a mai kula da siyasar wajen tarayyar turai ta bayyana a taron matasan Europe da masar cewa, muslunci a matsayin addinin da baya nuna wariya ga mutane.
Ta ce saboda haka ne ma kur’ani mai tsarki yake kira zuwa ga girmama dan adam da kuma kare hakkokinsa.
Dangane da matsayin alaka tsakaninsu da misrawa kuwa, ta bayyana cewa alaka ce ta tarihi wadda ta dade, kuma wanann alaka za ta ci gaba a hakan.
A bangaren batun yaki da ta’addanci kuma ta bayyana cewa, za su hada karfi da karfe da Masar domin yaki da ta’adanci ba kakkautawa.
Ta ce babbar manufarsu tare da kawayensy ita ce tabbatar da tsaro da aminci ga al’ummominsu da sauran al’ummomin suniya, saboda haka ba za su bar yan ta’adda su yi wasa da su.
3443476