IQNA

Za A Gudanar Da Tarukan Ranar Musulmi A Jahar Machost A Amurka

23:08 - November 08, 2015
Lambar Labari: 3444915
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wasu taruka masu taken ranar musulmi a garin Boston na jahar Machost a kasar Amurka a karon farko.


Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na «Boston MYP» cewa, dukkanin musulmin jahar Machost za su taru a babban ginin majalisar dokokin jahar.

Dukkanin masu taron za su hadu tare da wasu daga cikin ‘yan siyasar kasar daga wanann jaha domin gudanar da wadannan taruka, da hakan ya hada da yan majalisa na jahar domin kara tabbatar da fahimtar juna tsakanin musulmi da sauran al’ummomin.

Wannan dai shi ne karon farko da ake gudanar da irin wannan taro a kasar Amurka baki daya, wanda kuma ake ganin zai zama tamkar wani digon dan ba ne ga sauran jahohi domin bayar da dama ga mabiya addinin muslunci da su gudanr da addininsu cikin yanci.

Shirin dai za a fara shi nedaga karfe 10 na safe har zuwa karfe 2 na rana.

Dukaknin kungiyoyin musulmi na wannan jahar dai sun nuna cikakken goyon bayansu tare da bayyana aniyarsu ta halarta ba tare da wani bata lokaci ba, kamar yadda kuma wasu daga mabiya addinin kirista za su halarci taro.

3444625

Abubuwan Da Ya Shafa: amurka
captcha