Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na tashar talabijin ta Al-alam cewa, Sheikh Ali Salman ya bayyana cewa dukkanin abin da ake tuhumarsa da shin a neman canja tsarin kasar bas hi da tushe balantana makama, abin da yake kira shi ne a yi gyara
A nasu bangaren mahukuntan kasar Bahrain sun dage shari’ar babban sakataren jam’iyyar Al-wifaq jam’iyyar siyasa mafi girma a kasar har zuwa sha hudu ga watan gobe mai kamawa.
Tawagar lauyoyi masu kare sheikh Ali Salman sun bayyana cewa kotun masarautar Bahrain ta dage sauraren shari’ar ne saboda abin da ta kira rashin cikar bangarorin shari’ar da ya kamata su halarci zaman daga bangaren masu shigar da kara, wanda a cewar lauyoyin hakan na nuni ne da wata makida da ake shirin shiryawa a shari’ar.
Tun a cikin watan Fabrairun farkon wannan shekara ne dai mahukuntan kasar Bahrain suka kame Sheikh Ali Salman.
An kame shi ne bisa hujjar cewa yana sukar salon mulkin masarautar kasar tare da neman a gudanar da zaben ‘yan majalisa da zata hada dukkanin bangarori na syasa da al’ummar kasar, da kuma neman a samar da kundin tsarin mulki a kasar, wanda ‘yan majalisar za su rubuta.
Babban sakataren majalisar dinkin duniya da ma wasu kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa, sun kirayi masarautar Bhrain da ta gaggauta sakin Sheikh Salman ba tare da wani sharadi ba, domin kuwa ana tsare da shi ne kawai saboda dalilai na siyasa.
3447473