Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Reauters cewa, Ban Ki Moon ya bayn harin na ta’addanci da cewa ban takaici ne da bakin ciki, ya kuma mika sakon ta’aziyya ga wadanda abin ya shafa.
A daya bangaren kuma a al’ummomin duniya na ci gaba da yin Allawadai da kakkausar murya dangane da harin ta’addancin da aka kai dare jiya birnin Beirut na kasar Lebanon, wanda yay i sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 40.
Jamhuriyar muslunci ta bayyana wannan harin da cewa aiki ne na ta’addanci, wanda kuma yake nuna hakikanin matsayin wadanda suke dauke da irin wanann akida da kuma yadda suke kallon dan adam da rayuwarsa.
A nata bangaren majalisar dinkin duniya ta bayyana hakan da cewa aiki ne na dabbanci,
kamar yadda cibiyoyin addini sukaa bayyana cewa masu aikata irin wannan aiki sun yi nisa daga koyarwar addinin muslunci, kamar yadda fitattun ‘yan siyasa da malaman addini a ciki da wajen kasar ta Lebanon suka bayyana hakan da cewa aiki ne na ta’addanci tare da yin Allawadai da hakan.
Kungiyar ‘yan ta’adda ta ce ita ce ke da alhakin shirawa da kuma kai dukkanin hare-haren biyu na kunar bakin wake, wanda yay i sanadiyyar mutuwar fararen hula fiye da 43, tare da jikkatar wasu fiye da 240 sakamakon hare-haren.