Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Almanar cewa, a jawabin da ya gabatar a daren jiya, babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah yab bayyana cewa, harin Beirut da na Paris abin yin Allawadai ne, tare da bayyana cewa ya zama wajibi a tunkari ta’addancin yan ta’adda.
Daga abinh da ‘yan ta’addan daesh suka yi a cikin kasar Lebanon, ya kama a ce mutanen kasar sun gane su wane wadanann mutane, kuma ya kamata su gane dalilain da ya jawowa faransa a binda ya same ta, domin kuwa yan ta’addan daesh bas u da aboki, idan akwai wanda yake jin cewa saboda shi yan ataimaka ma ‘yan ta’addan Daesh domina yaki wadanda yake husuma da su a Syria koa wani wuri na daban to yana kure, domin kuwa abin da ya faru kan faransa ya isa ya zama babban darasi ga kowa.
Yaki Da Ta’addanci Na Bukatar Yin Amfani Da Hankali
Dangane da babbar manufar wadannan ayyuka na ta’addanci da yan kungiyar Daesh suke aikatawa kuwa, Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa dole ne a yi amfani da hankali matuka domin fuskantar wanann lamari, domin kuwa wadannan yan ta’adda akwai mai burka su.
Idana ka yi la’akari da irin ayyukan da suke yi a yankin baki daya, za afahimci cewa suna babban kawance da haramtacciyar kasar yahudawa, domin kuwa abin da suke yi duk yana a kan manufa guda ne, shi ne rusa kasashen musulmi da na larabawa baki daya.
3449523