IQNA

An kame Wasu Mata ‘Yan Ta’addan Daesh A Tunisia

22:40 - November 18, 2015
Lambar Labari: 3454434
Bangaren kasa da kasa, ma’aikatar harkokin cikin gida akasar Tunisia ta sanar da kame wasu mata 7 ‘yan ta’addan Daesh.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya bakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-alam cewa, bayanin ma’aikatar harkokin cikin hidan kasar ta Tunisia ya bayyana cewa dukaknin matan guda 7 sun amsa cewa s ‘yan ta’addan Daesh ne, kuma sun tasirantu ne da dan ta’adda Kamal Rizq wanda ya tsere.

Tashar talabijin ta Alhurrah ta bayar da rahoton cewa ta nakalto daga ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Tunisia cewa matan sun ce suna aiki ne karkashin kungiyar yan ta’adda ta Ansaru Shari’ah.

Matan sun kara da cewa kafin wannan lokacin sun kasance tare da kungiyar yan ta’adda ta Jundu Khilafah kafin daga bisani su hade da babbar kungiyar yan ta’addanci ta duniya.

3453766

Abubuwan Da Ya Shafa: tunisia
captcha