IQNA

Malaman Musulmi Sun Soki Qardawi Dangane Da Sabuwa Fatawarsa

21:14 - December 04, 2015
Lambar Labari: 3459731
Bangaren kasa da kasa, malaman musulmi da dama gami da masa sun soki Yusuf Qardawi dangane da sabuwar fatawar da ya bayar domin kare gwamnatin Turkiya da tattalin arzikinta.


Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na A-naba cewa, Yusuf Qardawi ya fitar da sabuwar fatawarsa domin kare manufofin gwamnatin Turkiya wadda ta baiwa malamai da masana da dama a duniya mamaki.

Da dama daga cikin malaman musulmi sun ce wannan fatawa da Qardawi ya fitar da kare jam’iyyar siyasa ce kawai, kuma ba ta da wata alaka da addinin muslunci, domin kuwa batu na ra’ayin siyasa kawai.

Malaman sun yi kakkausar suka mutumin wanda bai boye maitarsa ba wajen kokarin kare gwamnatin Trkiya dangane da tabargazar da take tafkawa wanda hakan ya zubar da musluncinta  aduniya, musamman ma taimakon yan ta’adda da take yi.

Qardawi ya kwatanta shugaban Turkiya Erdogan da annbi Musa (AS) tare da yin kira ga musulmi da su tsaya tare da Turkiya su kare tsarinta da tattailin arzikinta, inda har ma yake cewa yin hakan ya zama wajibi na shari’a a mahanrsa, lamarin da ya bakanta wa da dama daga cikin malamai masu ‘yanci a duniya, tare da bayyana hakan a matsayin wani salon wasa da addini.

3459684

Abubuwan Da Ya Shafa: Qardawi
captcha