IQNA

An hana Malaman Addini Shiga Harkokin siyasa A kasar Bahrain

23:21 - December 08, 2015
Lambar Labari: 3461371
Bangaren kasa da kasa, an hana malaman addinin muslunci mabiya tafarkin iyalan gidan manzo siga harkokin siyasa a kasar Bahrain.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Press TV cewa, a cikin wani bayani da mahukuntan kasar Bahrain suka fitar sun sanar da hana malamai shiga harkar siayasa.

Majalisar dokokin kasar wadda masarautar kasar take kafawa ce ta sanar da kafa wannan doka tare da tilasta yin aiki da ita  atsakanin al’ummar kasar.

Wannan majalisa dai wadda ba al’umma ne suka zabe ta, ita ke kokarin kirkiro doka tare da kafa kan al’umma, wanda kuma hakan kan zama daga cikin abin da mutanen suke nuna rashina mincewa da shi.

Tun bayan da al’ummar Bahrain ta fara bore tare da nuna rashin amincewa da salon mulkin mulukiya na kasar, aka fara daukar matakai na murkushe su, ta hanyar kawo sojoji daga kasasehn ketare domin hana su ci gaba da neman hakkokinsu nay an kasa.

Yanzu haka dai a kwai daruruwan fursunonin siyasa da suke tsare a kasar, wadanda aka kame su saboda rayoyinsu an siyasa, wanda kuma kungiyoyin kare hakkin bil adam na kasa da kasa suke yin kakkausar suka a kansa.

Sheikh Ali Salman na daga cikin wadanda ake tsare da su a kasar saboda dalilai na siyasa yanzu haka.

3460899

Abubuwan Da Ya Shafa: bahrain
captcha