IQNA

Ma’aikata Suna Da Lokacin Zuwa Sallar Juma’a A Turkiya

16:48 - January 06, 2016
Lambar Labari: 3480031
Bangaren kasa da kasa, Ahmad Dawud Auglo ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta mika wani daftarin kudiri domin neman baiwa ma’aikata damar zuwa salla.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Türkiye Gazetesi cewa, Ahmad Dawud Auglo firayi ministan kasar Turkiya ya bayyana a lokacin da yae Magana a gaban majalisar dokokin kasar cewa, gwamnatinsa za ta mika wani daftarin kudiri domin neman baiwa ma’aikata damar zuwa sallar Juma’a a kowane mako.

Dawud Auglo y ace a owane lokaci ma’akata suna kokawa kan karancin lokaci na zuwa gudanar da sallar Juma’a, a kan y ace daga wanann lokaci gwamnatinsa zata mika wani daftarin kudiri ga majalisa, idan aka amince da shi, to ma’aikata za su daar in aikinsu.

Haka nan kuma ya kirayi limaman masallatan Juma’a da cewa su rage yawan dogayen raka’oi a lokacin sallar, domin hakan zai bayar da dama ga masu larurori su samu sallar kuma su koma zuwa ga ayyukansu ba tare da wani tsaiko ba, kamar yadda yay i kira ga sauran ma’aikata da su yi amfani da damar ta hanyar da ta dace.

Firayi ministan na Turkiya ce bias ga dokokin kasar kowa yana hakkin ya gudanar da addininsa kamar yadda yake ganin ya yi daidai da maganrsa da kuma akidarsa.

http://iqna.ir/fa/news/3465226


captcha