IQNA

Dan Shahid Nimr: Akidar Daesh Da Al Saud Duk Abu Daya Ne

22:34 - January 20, 2016
Lambar Labari: 3480059
Bangaren kasa da kasa, dan shahid Sheikh Nimr ya bayyana cewa akidar Daesh wadda ta ginu a kan wahabiyanci da kuma Al Saud duk abu guda ne.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alalam cewa, Muhammad Nimr a zantawarsa da tashar BBC ya bayyana cewa, kawancen Amurka da Birtaniya da masarautar Al Saud zai cutar da wadannan kasashe daga bisani.

Ya ci gaba da cewa wadannan kasashe bai kamata su dubi gajeruwar alakarsu da masarautar Al Saud ba, su manta da cutar da hakan zai jawo ma al’ummominsu na har abada ba, domin kuwa alakarsu da wannan masarauta takaitattace da ta kafu a kan maslaha kawai, da zaran maslahar ta kare shi Kenan.

Muhammad Nimr ya ce wannan gidan sarauta na Al Saud shi ne tushen duk wani ta’addanci a duniya, domin su ne suka kafa kungiyoyin ta’addanci irin su Daesh da sauransu a duniya, kuma bisa akidar wahabiyanci da wannan masarauta ta ginua kansa ne aka gina a kidar ta’addanci a duniya.

3468878

captcha