IQNA

Azhar Bata TabaZama wajen gaba Da Mazhabar Shi’a Ba

23:25 - March 10, 2016
Lambar Labari: 3480217
Bangaren kasa da kasa, Muhammad Mahna mataimakin babban malamin cibiyar Azhar ya bayyana cewa maganar Ahmad Tayyib kan batun neman a gudanar da zama tsakanin malaman sunna da shi’a tana nan daram.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Yaum Sabi cewa, Muhamamd Mahna a tattaunawa ta wayar tarho da tashar Alhayat ya bayyana cewa, sheikhul Azhar ya sake jadda kiransa gudanar da zama tsakanin malaman sunna da shi’a na duniya baki daya.

Ya ci gaba da bat aba samun wani lokaci da cibiyar Azhar ta zama wajen yaki da wata mazhaba ko fahimta ba,a kan haka kuma ba zata taba yarda hankoron da wasu ke yi ba a halin yanzu na neman haifar da rikicin mazhaba a tsakanin musulmi ba.

Haka nan kuma ya kara da cewa ana koyar da akidu, kuma hakan ya hada da akidu na dukkanin bangarorin musulmi da suka hada da shi’a, haka nan kuma ana koyar da tarihi da sauransu na kowane bangare.

Malamin ya ce Azhar ba ta kiyayya da shi’a kuma za ta ci gaba da rike wannan matki nata ba tare da la’akari da matakin da wasu suke dauka ba, domin hakan yana tattare da hadari.

3482075

captcha