IQNA

17:41 - March 30, 2016
Lambar Labari: 3480276
Bangaren kasa da kasa, an fitar da wani littafi a kasar Masar da ke magana kan mahangar muslunci dangane da zaman lafiya tare da wadada ba musulmi ba, musamman ma mabiya addinin kirista.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ma'aikatar kula da harkokin addini a kasar Masar ce ta fitar da littafin, wanda yake kawo bayanai da hujjoji kan yadda musulunci yake mu'amala da mabiya addinin kirista, da kuma wajabcin zaman lafiya tare da su kamar yadda manzo ya yi tare da su.

Muhammad Mukhtar shi ne minista mai kula da harkokin addini a kasar, wanda kuma shi ne ya jagoranci kaddamar da littafin, inda ya bayyana cewa, a kowane lokaci musulunci addini ne na hankali da kyawawan dabiu da kuma girmama dan adam, kamar yadda kuma akwai bayanai da suke wajabta ma musulmi ma har su kare majami'oin mabiya addinin kirista idan bukatar hakan ta taso.

Ya ce akwai lamurra da dama da suke faruwa wadanda suke jawo rashin jituwa a tsakanin musulmi da kirista a kasar da ma wasu kasashen na daban, wanda kuma hakan bai cikin koyarwar duka addinin guda biyu.

Minista na kasar Masar ya ce dole ne musulmi da mabiya addinin kirista su zauna lafiya, su warware duk wasu matsaloli a tsakaninsu ta hanyar tattaunawa da fahimtar juna.

Kamar yadda ya yi ishara da cewa kada wani bangare ya nuna wa daya mummanr fahimta, domin kuwa za a iya samun bata gari a cikin kowane bangare, kuma addinin muslunci ya barranta daga ayyukan ta'addanci da ake dangata shi da su a wannan zamani.

3484962

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: