
Bangaren kasa da kasa, bayan kiran da wani daya daga cikin abin da ake kira kwamitin manyan malaman kasar Saudiyya mai suna Almanei ya yi kan yin mukabala a tsakaninsu da malaman shi’a daga bisani ya janye maganarsa.
Kamfanin dillanicn labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga jaridar Al-sabq ta kasar Saudiyya cewa, Sheikh Abdullah bin Salman Almanei daya daga cikin manyan malaman Saudiyyah ya bayyana kiran da ya yi na gudanar da mukabala a tsakanisu da malaman shi da cewa kiran bas hi da alaka da wannan kwami.
Ya ci gaba da cewa ya yi hakan ne da nufin kawo wani tunani wanda wata kila zai iya taimakawa a samu zama kan teburi tare da wadanda ya kira masu hankali daga cikin shi’a, domin yi musu bayani kan gaskiya, kuma a tabbatar musu da cewa kur’ani da sunna su kadai hanyoyi na tabbatar da dalili.
Bayan wannan furuci nasa ofishin daya daga cikin manyan malaman addini na kasar Ayatollah Makarim Shirazi ya mayar da martini da cewa, malaman Saudiyya ba a shirye suke su gudanar da tattaunawa tare da malaman shi ba, domin ita kanta wannan maganar wannan malamin na Saudiyya ya yi babu ladabi a cikinta.
Ya ce a duk lokacin da suka shirya malaman shi’a bas u da wata matsala ta zama kan teburin tattaunawa, amma su hanyoyin tabbatar da dalili da suka amince da su, su ne kur’ani da sunnar manzo da kuma hankali, domin kuwa akwai ayoyi saba’in a cikin kur’ani da suke tabbatar da cewa hankali daya ne daga cikin hanyoyi na tabbatar da dalili.
Almanei ya ce bayanan da aka yi ta watsawa akan cewa ya ce kwamitin malaman kasarsa ya bukaci a gudanar da irin wannan tattaunawa babu gaskiya a cikinsa.
A cewarsa a bin da ya ce kawai shi ne, yana da kyau a yi hakan in zai samu shi ma kmum aya kawo sharuddan da yake ganin ya kamata a ce sun samu kafin gudanar da irin wannan tattaunawa atsakanin bangarorin biyu.