IQNA

Taro Kasa Da Kasa Na Matasan Musulmi Da Kiristoci A Masar

23:53 - August 16, 2016
Lambar Labari: 3480717
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani zaman taro na matasan musulmi kan aiki tare wajen yada zaman lafiya da yaki da ta’addanci.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na sadal balad cewa, wannan taron cibiyar Azhar ce tare da hadin gwiwa da majalisar hadin kan majami’oin kiristoci na duniya ne suka dauki nauyin shirya shi.

An aike da goron gayyata ga matasan da za su harci taron su 40 ‘yan kasa da shekaru 30 daga kasashen turai da kuma nahiyar Afirka gami da yankin gabas ta tsakiya, da suka hada da maza da mata, inda za a gabatar da laccoci da kuma darussa na cikin aji kan yaki da ta’addanci.

Bayanin ya ce wannan taron zai tabo muhimamn battuwa da ya kamata mabiya addinan muslunci da kiristanci domin samun fahimtar kan batutuwa da dama da syka hada da yada tunanin sulhu da zaman lafiya a tsakanin al’ummomin duniya, da kuma earware matsaloli ta hanyar fahimta.

Sheikhul Azhar Ahamd Tayyib da kuma shugaban majami’ar kibtawa za su halarci wanann taro, tare da gabatar da jawabai.

3523285

captcha