Bayanin ya ci gaba da cewa a lokacin da aka bude gidan radiyon manyan makaranta na duniya wadanda 'yan kasar Masar ne irin su Abdulbasit Abdulsamad da su Musataf Isma'il da Muhammad Refat da sauransu, su ne suke gabatar da karatua cikinsa a hukumance.
Haisam Abu Zaid wanda fitaccen marubuci ne kuma masani kan harkokin addini da bincike kan abubuwan ad suke wakana, ya yi gargadin cewa ya gano wahabiyawa suna hankoron mamye wanann gidan radiyo, ta hanyar saka jama'arsu a cikin shirye-shiryensa.
Ya kara da cewa yanzu haka akwai yan kasar Saudiyya da suke gabatar da shirye-shirye a wannan gidan radiyo, kuma ba suna bin salon yadda aka tsara gidan radiyon ba ne kan mayar da hankali kana bin da ya shafi kur'ani da koyarwarsa, maimakon hakan suna tallar akidar wahabiyanci da kafirta musulmi ta hanyar wannan gidan radiyo, abin da ba a san hakan ba a shekarun baya.
Haka nan kuma dangane da hadarin da ke tattare da hakan, ya bayyana cewa idan ba a dauki matakin takawa wahabiyawan birki ba, wannan gidan radiyo zai tashi daga manufar kafa sa, zai koma wajen yada sabbin akidu masu haifar da fitina atsakanin musulmi na wahabiyanci da kafirta juna.
Yanzu haka wasu daga cikin masu gabatar wadannan shirye-shirye na radiyon kur'ania Masar fitattun daliban jami'ar Azahar ne, amma kuma wasunsu sun tasirantu da akidar wahabiyanci.