Bayanin ya ce a cikin shekara ta 2015 lamarin yafi yin muni matuka, inda ya kai kimanin kasha kasha 78 cikin dari na kymar ta karu.
Wannan dai sakamako ne ayyukan ta’addaci bisa akida wahabiyanci da ake aikatawa da sunan muslunc a duniya kamar yadda masana suka iya ganowa.
To sai dai kuma da dama daga cikin masu ‘yancin tunani da siyasa suna ganin cewa dukkanin abin da yake faruwa tare da sanin turawan ne, bil hasali ma su ne suka kirkiro duk wani aikin ta’addanci a duniya.
Hakan kuwa ya hada da karfafa akidar ta wahabiyanci a cikin musulmi tare da karfafa kasar da ta ke yada wannan aida a cikin duniyar musulmi domin ya zama hanyar ruguza musulmi da musulunc a idon duniya, kuma abin da yake faruwa kenan dai dai da abin da aka shirya.
‘Yan ta’adda masu dauke da akidar wahabiyanci suna kisan muuslmi fiye da wadanda ba musulmi ba a duniya, amma kuma a lokaci guda ana danganta su da abin da suke yi da musulci domin hakan dama shi ne babbar manufar.