IQNA

An Kashe Wata Musulma Mai Hijabi A Kasar Faransa

12:02 - September 26, 2016
Lambar Labari: 3480808
Bangaren kasa da kasa, an kashe wata mata musulma a kasar Faransa ta hanyar harbinta da bindiga a birnin Pantan.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya bayar da rahoton cewa ya nakalto daga shafin yanar gizo na kamfanin dillancin labaran Morocco cewa, an harbe matar ne a lokacin da take cikin tukin mota.

Wadanda suka ganewa idanunsu abin da ya faru dai sun bayyan acewa, wasu mutane ne da ba a san ko su wane ne ba suka yi harbin, inda suka kasha matar a lokacin da take tuki a cikin motarta tana sanye da hijabin musulunci.

Tuni dai jami’an ‘yan sanda suka ce sun fara gudanar da bincike kan lamarin domin gano wadanda suka tafka wannan mummunan aiki, tare da gurfanar da su a gaban kuliya.

Musulmin kasar Faransa dai mafi yawansu sun fito ne daga arewacin nahiyar Afika (kasha 35 daga Algeria, kasha 25 daga Morocco, kasha 10 kuma daga Tunisia) daga cikinsu akwai wadanda ma ba addinin ya dame su ba sun zama faransawa turawa, yayin da kuma wasu suna kamantawa wasu kuma suna wuce gona da iri, musamman bayan bullar akidar ta’addanci.

Masu kyamar musulmi a kasar ta Faransa dai ba su banbance tsakanin masu akidar ta’addanci wadanda su ne mafi karanci, da kuma sauran musulmi wadanda bas u yarda da wannan akida da ta yi hannun riga da musulunci ba, inda suke cutar da duk wanda ya amsa sunan musulmi.

3532661


captcha