Ya ce tun kimanin shekaru 25 da suka gabata ne aka bude wannan gidan radiyo, wanda yake gabatar da shirinsa kan lamurra da suka shafi kur’ani da kuma koyarwarsa, kafin daga bisani a bude bangaren talabijin wanda shi ma yake gabatar da irin wadannan shirye-shirye.
Daga cikin muhimman abubuwan da ake mayar da hankalia kansu shi ne yadda ya kamata musulmi su zauna da juna tare dasamun fahimta, da kuma zama lafiya da sauran mabiya addinai, kamar yadda musuunci ya koyar, haka nan kuma ana taba batutuwa da suka shafi tattalin arziki, zamantakewa, al’adu da sauransu, duk a mahanga ta addinin muslunci.