Bayanin y ace ko shakka babu abin da ake yi wa mabiya addinin muslunci saboda addininsu ya sabawa kaida da kuma dokokin kasar Amurka, akan mutane 530 daga cikin yan majalisar da kuma wasu masu fada aji a jahar sun rattaba hannu kan wannan wasika.
Georgia Kisser wata day ace daga cikin masu rajin kare hakkokin marassa rinjaye, ta bayyana cewa za su ci gaba da kare hakkokin musulmi da ake zalunta tare da cin zarafinsu ba dalili.
Tun daga lokacin da aka kaddamar da hari a wurin shakatawar yan luwadi a birnin Orlando, msuulmi suke fuskntar matsaloli na tsangwama a cikin birane da daman a kasar Amurka, wanda hakan ya sanya wasu suka fara tunanin daukar mataki na doka domin fuskantar lamarin, domin kuwa sau da dama agaban jami'an yan sanda ne ma ake kai musu hari ko cin zarafinsu, ba tare da jami'an tsaron sun yi komai ba.