Kamfanin
dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, tashar Press TV ta bayar da rahoton cewa, wata kotu a kasar
Bahrain ta bayar da umarnin baje kolin kaddaririn jam'iyyar Alwifaq a ranar 26
ga wannan watan Oktoba.
Umarnin kotun ya hada da kwashe dukkanin kaddarorin da ke babban ofishin jam'iyyar da ke birnin Manama, da kuma sauran ofisoshinta da ke cikin sauran yankunan kasar, gami da kudaden jam'iyyar da suke a bankuna da sauran kaddarori da suke da alaka da jam'iyyar.
Masarautar mulkin kama karya ta kasar Bahrain dai ta dauki wannan matakin ne biyo bayan kama babban sakataren jam'iyyar, wadda mafi yawan al'ummar kasar suke mara mata baya, bisa abin da mahukuntan suka kira barazanar da jam'iyyar ke yi ga masarautar kasar.
A kwanakin baya ne aka yanke hukuncin darin shekaru 4 a gidan kaso kan sheikh Ali Salman bababn sakataren jam'iyyar, kafin daga bisani kuma kotu ta kara wa'adin zuwa shekaru 9 a gidan kaso.