IQNA

Kyamar Musulmi Ta Karu Da Kashi 89 A Amurka

23:45 - October 23, 2016
Lambar Labari: 3480878
Bangaren kasa da kasa, Sakamakon wani bincike da aka gudanar a kasar Amurka ya nuna cewa an samu karuwar ayyukan laifi na kymar musulmi a kasar Amurka da kimanin kashi tamanin da tara.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, Tashar talabijin ta Press TV ta bayar da rahoton cewa, shafin jaridar Hafington Post ya sheda cewa, an gudanar da wani bincike da ya kunshi jahohi 20 na kasar Amurka da kuma birnin New York kan yadda ake aikata laifuka, inda binciken ya nuna cewa aikata laifuka ya karu da kashi 06%, yayin da kuma ayyukan laifi da suka danganci kyamar musulmi suka karu da kashi 89%.

Wadanda suka gudanar da binciken sun ce dalilin karuwar kyamar msuulmi a Amurka shi ne yadda masu akidar wahabiyanci da salafiyanci suke yin maganganu na tsatsauran ra'ayi kan wadanda ba musulmi ba, sai kuma abubuwan da suke faruruwa na ayyukan ta'addanci a cikin kasashen duniya, musammana Syria da wasu kasashen larabawa, inda 'yan ta'adda masu da'awar jihadi suke nuna hotunan kisan jama'a da suke yi ta hanyoyi na dabbanci da rashin imani, duk da sunan muslunci.

3539955


captcha