IQNA

23:44 - November 07, 2016
Lambar Labari: 3480917
Bangaren kasa da kasa, ana shirin gudanar da wani babban taro na kasa da kasa kan jihadi da sufanci a kasar Tunisia tare da hadin gwaiwa da jamhuriyar muslunci ta Iran.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na cibiyar yada al’adun muslounci ta Iran cewa, za a gudanar da wani babban taro na kasa da kasa kan jihadi da sufanci a kasar Tunisia tare da hadin gwaiwa da ofishin yada al’adu na Iran da ke kasar.

Taufiq bin Amir shi ne shugaban bangare nazari kan harkar sufanci a jami’ar birnin Tunis, ya zanta tare da shugaban ofishin kula da harkokin al’adu na kasar Iran da ke kasar Muhamamd Asadi Muwahhad kan batun shirin taron.

Babban abin da wannan taro zai mayar da hankali a kansa dai shi ne, mahangar addinin muslunci dangane da jihadi na gina ruhi da kuma sufanci, wanda ya hada da yadda musulmi zai tsarkake ruhinsa tare da damfara shi da Allah madaukin sarki.

Sufanci dai ita ce tsarke zuciya daga duk wata dauda ta sabon Allah, da kuma lizimtar ambaton Allah da kiyaye haninsa da bin umarninsa, da yin ibada domin kara samun kusanci da Allah madaukakin sarki.

Kasar Tunisia dai tana daga cikin kasashen larabawan Afirka da suka yi nisa a wajen karafafa harkar sufanci da zikirin ubangiji.

3544163


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: