IQNA

20:16 - November 09, 2016
Lambar Labari: 3480922
Bangaren kasa da kasa, jami’an huldar diflomasiyya na kasashen tarayyar turai sun bukaci a kawo karshen killace yankin zirin gaza da Isra’ila ke yi.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na Jordan Times cewa, tawagar Jakadun kasashen kungiyar tarayyar turai daga kasashe daban-daban ne suka ziyarci yankin zirin Gaza a jiya, inda suka nuna damuwa matuka dangane da halin da al’ummar wannan yanki suke ciki.

Jakadun sun yi kira ga haramtacciyar kasar Isra’ila da gaggauta kawo karshen killace yankin zirin gaza da take yi tsawon shekaru, tare da haramta al’ummar wannan yanki yin rayuwa kamar sauran al’ummomin duniya.

Jami’an tarayyar turai 45 ne da suka hada shugabannin ofisoshin jakadanci na kasashen kungiyar da ke kasashen duniya daban-daban, inda suka gana da jama’a da iyalai a yankin zirin Gaza, tare da jin ta bakinsu kan irin halin da ske ciki.

Daga ciki akwai wakilai na kasashen Sweden ,Malata, Salvania, Danmark, Ireland, Lutuania, Finland, Holland, Poland, Spain, Belgium, jamus, Cyprus, Italia, Girka da kuma Portugal.

Wannan ita ce tawagar kungiyar tarayyar turai ta farko da ta ziyarci Gaza tun bayan harin Isra’ila a yankin na shekara ta 2014, inda yahudawan sahyuniya suka kasha fararen hula fiye da dubu a yankin.

Tun a cikin shekara ta 2007 ce haramtacciyar kasar Isra’ila ta kakaba takunkumi a kan yankin baki daya har zuwa.

3544657


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: