IQNA

22:54 - November 16, 2016
Lambar Labari: 3480945
Bangaren kasa da kasa, kungiyoyin kare hakkin bil adama sun ce har yanzun jami'an tsaron kasar Myanmar suna ci gaba take hakkin musulman Rohinga na kasar.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin Islamic News cewa, baya ga jami'an tsaro masu tsatsauran ra'ayin addinin buda sun kona gidagen musulman yan Rakhin da dama. Banda haka a wani bangaren jami'an tsaron kasar ta Myanmar sun budewa wadan nan masu tsatsauran ra'ayin addini wurare don kissan musulman na kabilar Rohinga. Kamar yadda suka sukan kashe musulman tare da tuhumarsu da ayyukan ta'addanci da kuma alaka da yan ta'adda daga wajen kasar.

Majiyar labarai daga yankin na Rashin sun bayyana cewa sojojin kasar ne suke budewa masu tsatsaurar ra'ayin addini hanyoyi da kuma damar kona gidajen musulman Rohinga.

Sai kuma a bangaren gwamnatin kasar wacce taki amincewa da yan kabilar ta Rohinga a matsayin yan kasa don haka basa da hakkin samun kome daga bangaren gwamnatin kasar wadanda suka hada da karatu da kula da lafiyan. Musulman kasar ta Myanmar dai sun kasance cikin takurawa na jami'an tsaron kasar da kuma masu tsatsauran ra'ayin addinin na fiye da shekaru 4 da suka gabata.

Sannan wani abin mamaki shi ne duk abubuwan da suke faruwa a cikin yan shekaru da suka gabata suna faruwa ne a idon jam'iyyar mai riya kare hakkin nbila'adama wacce take da rinjaye a majalisar dokokin kasar ta Myanmar.

Wanann lamari dai ya harzuka da dama daga cikin al'ummar musulmi a duniya, yayin da wasu daga cikin gwmnatoci masu 'yancin siyasa kuma suka yi Allah wadai da hakan.

3545755


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: