IQNA

23:24 - November 19, 2016
Lambar Labari: 3480954
Bangaren kasa da kasa, Iraniyawa mazauana kasar Tanzania suna gudanar da tarukan arbaeen na Imam Hussain.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, mutanen kasar Iran da suke zaune a kasar Tanzania sun gudanar da tarukan arbaeen a gidan jakadan kasar Iran da ke birnin Darussalam fadar mulkin kasar.

Haka nan kuma ana gudanar da irin wadannan taruka a tsibirin Zanzibar a masallacin Alghadir, tare da halartar mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah da ma sauran jama’a musulmi.

Rahoton ya kara da cewa bisa ga alada ana gudanar da irin wadanna taruka a masallacin yan Khoja, kuam acikin wadannan kwanaki taron yana samun halartar jama’a masu tarin yawa.

Za a ci gaba da gudanar da tarukan har zuwa karshen watan Safar, wanda zai hadu da lokacin tunawa da rasuwar ma’aiki (SAW) da kuma shahadar Imam Hasan Almujtaba (AS) da kuma shahadar Imam Ridha (AS).

3547212


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: