IQNA

22:44 - November 20, 2016
Lambar Labari: 3480957
Bangaren kasa da kasa, kamfanonin da ke gudanar da ayyukan yawon bude ido a kasar Iraki sun taimaka da motocin bus fiye da 200 na daukar masu ziyarar arbaeen.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, bangaren kula da huldar jamaa na hubbaren Iamm Hussaini (AS) ya tabbatar da cewa, kamfanoni amsu kansu da suke gudanar da ayyuka na yawon bude ido da ziyara a Iraki sun taimaka matuka da dukkanina bin da ke hannunsu domin hidima ga masu ziyarar arbaeen.

Ya ce an yi amfani da kayansu da suka hada da motoci da wurare da sauransu kyauta, duk saboda hidima ga masu ziyara, wanda hakan yana amatasayin babbar sadaukarwa.

Daga cikin wurare da aka yi ta daukar masu ziytara ana kaisu birnin Karbala akwai Najaf, sai kuma bagadaza da kuma Basara, da sauran wurare wadanda suke da iyaka da kasar Iraki da wasu kasashen.

Abin tuni a na dais hi ne, fiye da yan kasashen ketare miliyan 3 ne suka gudanar da aikin ziyarar arbaeen a wannan wannan shekara, yayin da Irakawa kuma sun haura miliyan goma sha shida.

3547379


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: