IQNA

21:05 - November 30, 2016
Lambar Labari: 3480987
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da sallah hadin kai da kuma jerin gwano domin tunawa da wafatin manzon Allah (SAW) a tsibirin Zainzibar.
Kamfanin dillanicn labaran kur'ani na iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren hulda da jama'a na cibiyar yada aladun muslunci cewa, an gudanar da wannan taro da jerin gwano ne a tsibirin na Zinzibar, wanda ya samu halartar mabiya mazhabar shi'a da kuma 'yan Sunnah.

Wannan taro dai ya gudana ne a Husainiyar mutanen Bahrain domin tunawa da bakin cikin da ahlul bait suka samu kansu a ciki sakamakon yadda lamurra suka kasance tare da su, bugu da kari kan hakan tunawa da wafatin manzon rahma (SAW) wanda ya zo a daidai wannn lokaci.

An gabatar da jawabai a wurin, daga cikin wadanda suka jawabi har da sheikh Jalal daya daga cikin malaman makarantar Hauza ta Imam Sadiq (AS).

A cikin bayanin nasa ya kawo tarihin amnzon Allah (SAW) da kuma wasu daga cikin irin darussa da ke a cikin wannan rayuwa tasa mai albarka, da kuma yadda za mu dauki wadannan darussa domin yin aiki da su a cikin rayuwarmu ta yau da kullum.

Daga cikin irin wadannan darussa da rayuwar manzo take koyar da mu kuwa har da zaman lafiya da tausayin dan adam da taimaka masa, da kokarin yada dabiu masu kyau a cikin al'umma domin kyautata rayuwarta ta zamantakewa, da dai sauran darussa wadanda rayuwarsa mai albarka take koyar da yan adam baki day aba musulmi kawai ba.

3550041


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: