IQNA

Masallaci Mafi Jimawa Da Iraniywa Suka Gina A Gabshin Afirka

21:19 - December 07, 2016
Lambar Labari: 3481011
Bangaren kasa da kasa, masallacin Kizimkazi shi ne masallaci mafi jimawa da Iraniyawa suka gina a tsibirin Zanzibar a lokacin mulkin sarakunan Shiraz a watan Zilkada hijira ta 500 kamariyya, 1107 miladiyya.

Morteza Rezvanfar wani masani kan harkokin tarihi kuma mai gudanar da bicike kan wuraren tarihi, a zantawarsa da IQNA ya bayyana cewa, wannan wuri yana da tsohon tarihi, domin ginin masallacin ya kai shekaru 938 a halin yanzu.

A kicin harabar masallacin an saka wani allo wanda yake dauke da tarihin ginin masallacin, wanda aka bayyana cewa an gina shi a cikin shekara ta 500 na hijira kamariyyah, wanda ya yi daidai da shekara ta 1107 shekarar miladiyya.

Wannan masallacin dai an bashi sunan Fatima Zahra (SA) wanda kuma har yanzu shi ne sunansa a rubuce, amma sakamakon shudewar zamani an rika danganta shi da sunan yankin da yake.

Jama’a sunan gudanar da sallolinsu akowace rana acikin wannan masallaci, kuma a halin yanzu ana kallonsa amatsayin daya daga cikin wuraren tarihi da k cikin wannan tsibiri, haka nan kuma kasar Tanzania na kallonsa a matsayin muhimman wurin tarihi na kasa.

Wasu bayanai na tarihi sun ce sarkin lokacin ya kasha mutumin da ya gina wannan masallacin a wancan lokacin mai suna Kizi, kuma an runfeshi a kusa da wurin, wanda hakan ya sanya yanzu akwai wata makabarta da take gefen masallacin inda kabarin mutumin yake.

3552006

captcha