IQNA

Manyan Malam Tijjaniya Daga Senegal Za Su Kawo Ziyara A Iran

22:46 - December 14, 2016
Lambar Labari: 3481034
Bangaren kasa da kasa, wata tawagar manyn malam darikar Tijjaniya za su kawo ziyara a kasar Iran daga kasar Senegal karkashin jagiran Sheikh Ahmad Nyas.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin yada labarai na hukumar yada al'adun muslunci cewa, nan mako guda mai zuwa wata bababr tawaga ta mabiya darikar Tijjaniya za ta kawo ziyara a kasar Iran daga kasar Senegal, domin karba goron gayyata na cibiyar Ahlul bait (AS) ta duniya.

Babbar manufar wannan ziyara dai it ace kara samar da hadin kai a tsakanin musulmi mabiya darikun sufaye da kuma mabiya tafarkin ahlul bait, wadanda dukkaninsu sun hadu a kan haka.

Sheikh Ahmad Nyas shi ne bababn malamin darikar Tijjaniya a kasar Senegal, wanda kuma yana da martaba a idanun dukaknin mabiya wannan darika a duniya, musamman a kasashen da mabiyan darikar suka fi yawa, wato Senegal, da kuam Najeriya gami da Guinea, sai kuma kasashen turai da Amurka.

3554012


captcha