IQNA

Indiyawa Sun Yi Zanga-Zangar Goyon Bayan Musulmin Kasar Myanmar

22:56 - December 21, 2016
Lambar Labari: 3481057
Bangaren kasa da kasa, Dubban Indiyawa ne suka gudanar da jerin gwano a birnin New Delhi domin nuna goyon bayansu ga musulmin kasar Myanmar da ake yi wa kisan kiyashi.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, shafin Arakan ya bayar da rahoto daga birnin New Delhi cewa, dubban mutane suka gudanar da wannan jerin gwano, wanda ya hada da kungiyoyin farar hula, da na kare hakkin bil adama da sauran jamar gari, domin Allawadai da kisan gillar da ake yi wa musulmi 'yan kabilar Rohingya a kasar Myanmar.

Rahoton ya ce masu zanga-zangar sun yi gangami a gaban babban ofishin majalisar dinkin duniya a kasar India wanda yake a birnin na New Delhi, inda suka yi kira ga majalisar dinkin duniya da ta safke nauyin da ya rataya akanta na kare rayukan fararen hula musulmi da ake kashewa a kasar Myanmar saboda su musulmi ne.

Haka nan kuma sun yi Allawadai da rashin daukar kwararan matakai daga bagaren majalisar dinkin duniya da ma sauran kasashe masu raya kare hakkin bil adama, kan rashin taka wa gwamnatin Myanmar birki a kan wannan ta'asa da sojojinta gami da 'yan addinin Buda suke aikatawa a musulmi marassa rinjaye a kasar.

Gwamnatin kasar Myanmar dai tana bayyana 'yan kabilar Rohingya wadanda mabiya addinin muslunci ne a matsayin bakin haure, wadanda suka shigo kasar daga kasar Bangaladash daruruwan shekaru da suka gabata.

3555250


captcha