IQNA

Amman Birnin Al'adun Muslunci Na Wannan Shekara

22:51 - December 25, 2016
Lambar Labari: 3481067
Bangaren kasa da kasa, ana gudanar da bukukuwan murnar sanar da birnin Amman na kasar Jordan a matsayin birnin al'adun muslunci na duniya a 2017.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin Jordan Times cewa, a cikin wannan shekara mai karewa ta 2016 ne aka sanar da kasar Jordan mai daddaen tarihin muslunci a mtsayin kasar da za ta rike wannan matsayi.

An bayyana birnin Aman fadar mulkin kasar a matsayin birnin da ya fi dacewa da matsayin birnin aladun muslunci na duniya, kamar yadda kuma masautar kasar take danganta kanta da gidan hasimawa dangin amnzon Allah (SAW) tun da jimawa.

Kamar yadda kasar take da tarihi ta fuskar addinin kiristanci, domin kuwa a baya ma a cikin shekara ta 1920 an ajiye dutsen sakhra a kasar, kuma mabiya addinin kirista da dama suna danganta kansu da kasar tun bayan fakuwar annabi Isa (AS).

Kasar Jordan dai a halin yanzu tana daga cikin kasashen larabawa da suke da tsari irin na sarauta, kamar yadda yadda wasu daga cikin kasashen yankin tekunfasha suke da irin wannan tsari.

Sai ita kasar Jordan tsarin nata ya sha banban, domin kuwa tana bin salon muki ne wanda ya yi kama da na turawa, sabanin sarakunan larabawan yankin tekunfash wadanda suke bin salon mulki na al'ada da suka gada tun daga yanayi na dabi'ar larabawan kauye.

Haka nan kuma birnin mashhad ma an bayyan shi a wannan matsayi daga cikin biranan da ban a larabawa ba, sai kuma Kampala daga Uganda wato daga nahiyar Afirka, wanda ISESCO ce take daukar nauyin ayyana birnin al'adun muslunci.

3556379


captcha