IQNA

19:12 - February 02, 2017
Lambar Labari: 3481195
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin jahohin Amurka da suka hada har da Washinton, New York da kuma Virginia sun nuna rashin amincewarsu da shirin Trump na korar baki da musulmi.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, jaridar Independent ta bayar da rahoton cewa, bayan kotun koli ta jahar Washinton ta sanar da rashin amincewarta dangane da shirin Trump na hana musulmi daga kasashe7 da kuma ‘yan gudun hijira shiga Amurka, wasu jahohin ma sun dauki irin wannan mataki.

Mora Hilly daya daga cikin manyan alkalai a kasar Amurka ta bayyana cewa, wannan mataki na Trump ya sanawa dukkanin kaidoji da dokoki na kasa da kasa da kuma na kasar Amurka, a kan haka ba za su taba amincewa da shi ba, domin kuwa ya ginu ne akan nuna wariya da bangaranci.

Mark Herring shi ne babban alkalin alkalai na jahar Virginia ya bayyana cewa, akawi musulmi da dama da suke cikin wannan jaha wasu ma’aikata ne wasu kuma daliban jami’a ne, yanzu kuma da suka tafi hutu suna cikin matsala domin sun kasa dawowa kasar, saboda wannan doka ta Trump.

Eriak Shiderman shi ne babban alkalin alkalai na gundumar New York, ya bayyana cewa wannan mataki na Trump ya yi hannun riga da dokokin Amurka da kuma ‘yan adamtaka,a kan haka ba za su yi aiki da wannan doka ba.

A farkon wannan mao San Francisco ta sanar da shigar da kara a kan wannan kudiri na Trump a kan musulmi da ‘yan gudun hijira.

3569560


Abubuwan Da Ya Shafa: IQNA ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Trump ، New York ، Washington ، Virginia ، Amurka ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: