IQNA

23:05 - February 11, 2017
Lambar Labari: 3481222
Bangaren kasa da kasa, kotun daukaka kara ta tarayya a kasar Amurka ta hana maido da dokar nan da Trump ya kafa ta hana baki shiga cikin kasar Amurka.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, ya nakalto daga Press TV cewa, Shugaban Amurka Donald Trump ya sake fuskantar koma baya a kokarinsa na haramta wa 'yan wasu kasashen musulmi bakawai shiga Amurkan, bayan wata kotun daukaka kara ta tarayya a Amurkan ta yi watsi da karar da ya shigar na a dawo da wannan dokar bayan ta wata kotun ta soke ta a baya.

Rahoton ya ci gaba da cewa a hukuncin da alkalan kotun su uku suka yanke sun yi watsi da kiran da a dawo da dokar suna masu cewa babu wani dalili da gwamnatin Trump din ta gabatar da ke nuni da cewa tsaron lafiyar Amurkan na cikin hatsari da har za a bukaci soke hukuncin da kotun farko din ta yanke.

A ranar ashirin da bakwai ga watan Janairun da ya gabata ne dai shugaba Trump din ya sanya hannu kan wata doka da ta haramta wa 'yan wasu kasashe 7 na musulmi da suka hada da Iran, Siriya, Iraki, Libiya, Yemen, Sudan da Somaliya shiga Amurka har na tsawon watanni uku, lamarin da a ranar Juma'ar da ta gabata alkali wata kotun Amurkan mai shariaJames Robart ya soke ta da cewa dokar ta saba wa kundin tsarin Amurka.

Shugaba Trump dai ya fake ne da batun fada da ta'addanci wajen kafa wannan doka wacce ta ke ci gaba da fuskantar tofin Allah tsine a ciki da wajen Amurkan.

3572805


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: