IQNA

A Myanmar Sojoji Sun Bayyana Kisan Musulmi A Matsayin Kare Dokar Kasa

22:52 - March 01, 2017
Lambar Labari: 3481274
Bangaren kasa da kasa, Rundunar sojin kasar Myanmar ta bayyana kisan kiyashin da take yia kan musulmi 'yan kabilar Rohingya a matsayin kare dokokin kasar da tabbatar da tsaro.

Kamfanin dilalncin labaran IQNA ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran Reauters ya bayar da rahoton cewa, a karon farko rundunar sojin kasar Mayanmar ta mayar da martani dangane da zarginta da ake yi da yi wa musulmi 'yan kabilar Rohingya kisan kiyashi a kasar.

Babban hafsan hafsoshin sojin kasar ta Myanmar janar Miya Ton ya yi watsi da rahoton da kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya fitar, da kuma wanda kungiyar Amnesty Int ta fitar a makon da ya gabata, dangane da kisan kare dangin da sojoji suke yi kan musulmi a kasar tare da hadin gwiwa da 'yan addinin buda masu tsatsauran ra'ayi.

Janar din ya ce yana son duniya ta sani cewa, rahotannin da ake bayarwa kan kisan musulmi a kasar Myanmar ba su da tushe, domin kuwa sojoji suna yin aiki ne domin tabbatar da tsaro da kuma kare dokokin kasa, kuma bisa binciken da rundunar sojin kasar ta gudanar kan wannan rahoto, babu wani abu da ke tabbatar da gaskiyar abin da rahoton ya kunsa.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa sun nuna wasu daga cikin hotuna da aka dauka wasu daga cikinsu kuma hotunan tauraron dan adam ne, da ke nuna yadda sojojin Myanmr suke kashe musulmi da kuma kone musu gidaje da kaddarori.


3579618


captcha