Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga tashar alalam cewa, hukumomin makarantar sakadandare ta Johannes Rau a kasar Jamus ta hana dalibai musulmi yin salla a cikin makarantar.
A cikin bayanin da mahukuntan makarantar suka fitar sun bayyana cewa, yin alwalla da kuma yin salla a cikin wannan makaranta ya sabawa dokar makarantar, a kan duk wanda aka samu da karya wannan doka za a dauki mataki a kansa.
Haka nan kuma hukumomin makarantar sun umarci malamai da ma sauran dalibai da sun sanya ido domin gano wadanda suke yin alwalla ko kuma yin sallaa cikin dakuna ko kuma a wasu wurarea cikin makarantar domin daukar matakin ladabtarwa akansu.
Wannan batu ya dauki hankulan mau bin kafofin zumunta na yanar gizo, kuma, wasu daga cikin al'ummomin kasar ta Jamus suna ganin cewa matakin ya yi tsauri matuka, kuma yana amatsayin tauye hakkin wasu a kan addininsu.
Sai dai a nasu bangaren kungiyoyi da jam'iyyun siyasa masu tsananin adawa da addinin muslunci sun maraba da wannan mataki, inda suke ganin yin hakan ne kawai zai taka wa musulmi birki da kuma hana yaduwar muslunci a cikin kasar jamus.